Nigerian news All categories All tags
Abunda shugabannin jami'an tsaron Najeriya suka tattauna da Buhari

Abunda shugabannin jami'an tsaron Najeriya suka tattauna da Buhari

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a yau din nan ranar Alhamis, 25 ga watan Janairun shekara ta 2018 ya gana da shugabannin jami'an tsaron kasar a yunkuri da ake kallo kamar na dakushe tabarbarewa tsaron da ake fama da shi a ofishin sa dake a Abuja.

Mun samu dai cewa babban ministan tsaron kasar Mansur Dan-Ali ne dai tare da taimakon babban mai ba shugaban kasar shawara ta fannin tsaro Babagana Monguno suka yi wa jami'an tsaron jagora a taron.

Abunda shugabannin jami'an tsaron Najeriya suka tattauna da Buhari

Abunda shugabannin jami'an tsaron Najeriya suka tattauna da Buhari

KU KARANTA: Fasto zai dauki nauyin kowaya almajirai sana'a

Legit.ng haka zalika ta samu cewa sabon babban Daraktan hukumar leken asirin kasar Ahmed Abubakar ya samu halartar taron tattaunawar da ya wakana cikin sirri.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu yanzu-yanzu na nuni da cewa an rufe filin sauka da kuma tashin jiragen sama na kasa-da-kasa na tunawa da Nnamdi Azikwe dake a garin Abuja.

Mun samu dai cewa an rufe filin jirgin ne na dan wani lokaci biyo bayan wata 'yar tangarda da wani jirin yawo mallakin kamfanin Nest Oil ya samu yayin da yake kokarin sauka a yau din nan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel