Nigerian news All categories All tags
Gwamnatin tarayya za ta baiwa 'yan Najeriya 8m kulawar lafiya kyauta a 2018

Gwamnatin tarayya za ta baiwa 'yan Najeriya 8m kulawar lafiya kyauta a 2018

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, za ta gudanar da kulawar lafiya kyauta ga 'yan asali kuma mazauna al'umma miliyan takwas na kasar nan a tsakanin watan Afrilu da Dasumba na shekarar 2018.

Wannan goma ta arziki doriya ce akan gudanar da aikin tiyata kyauta ga marasa hali 10, 150 na kasar da gwamnatin ta dirfafa wajen aiwatarwa.

Ministan lafiya na Najeriya, Farfesa Isaac Adewole, shine ya bayyana hakan a wata ganawa da 'yan jarida bayan zaman majalisa da aka gudanar a ranar larabar da ta gabata.

Farfesa Isaac Adewole

Farfesa Isaac Adewole

Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari shine ya jagoranci zaman majalisar na sama da awanni biyar da aka gudanar a fadar shugaban ta birnin tarayya.

KARANTA KUMA: Jam'iyyar APGA ta amince da shugaba Buhari

Ministan wanda ya fara tantance wannan aiki a ma'aikatarsa tun shekarar 2016 ya bayyana cewa, gwamnatin shugaba Buhari za tayi wannan hobbasa ne domin tallafawa gajiyayyu da kuma marasa galihu na kasar nan.

Adewole ya gana da 'yan jarida a fadar ta shugaban kasa, inda ministan ruwa; Alhaji Suleiman Adamu, karamin ministan aikace-aikace; Alhaji Mustapha Shehuri tare da ministan noma da raya karkara; Mista Audu Ogbeh sun tofa albarkacin bakinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel