Nigerian news All categories All tags
Kayatattun hotunan Osinbajo, Dangote, Udoma, da Bill Gates, a wurin taron tattalin arzikin duniya

Kayatattun hotunan Osinbajo, Dangote, Udoma, da Bill Gates, a wurin taron tattalin arzikin duniya

- Ana gudanar da taron tattalin arzikin duniya (WEF) a Davos dake kasar Switherland

- Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo, ministan kasafi da tsare-tsare, Udoma Udo Udoma, da Aliko Dangote sun halarci taron

- Ana saka a gobe, Juma'a, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, zai gabatar da jawabi

Ana gudanar da taron kwanaki uku a garin Davos dake kasar Switzerland domin tattauna batutuwan tattalin arzikin duniya (WEF).

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Ministan kasafi da tsare-tsare, Udoma Udo Udoma, da Aliko Dangote, sun halarci taron.

Kayatattun hotunan Osinbajo, Dangote, Udoma, da Bill Gates, a wurin taron tattalin arzikin duniya

Osinbajo da Theresa May

Firaministan kasar Ingila, Theresa May, mataimakin shugaban kasar Afrika ta kudu, Cyril Ramaphosa, da sakataren kasashen duniya masu arzikin man fetur (OPEC) sun halarci taron.

Kayatattun hotunan Osinbajo, Dangote, Udoma, da Bill Gates, a wurin taron tattalin arzikin duniya

Osinbajo, Dangote, Udoma, da Bill Gates, a wurin taron tattalin arzikin duniya

Ana saka ran shugaban kasar Amurka Donald Trump zai gabatar da jawabi a wurin taron gobe, juma'a.

DUBA WANNAN: Fastocin Atiku dauke da wasu sakonni sun mamaye garin Lokoja

Trump shine shugaban kasar Amurka na farko a cikin shekaru goma da zai halarci taron.

Kayatattun hotunan Osinbajo, Dangote, Udoma, da Bill Gates, a wurin taron tattalin arzikin duniya

Osinbajo da mataimakin shugaban kasar Afrika ta kudu

Kasancewar sa attajiri tun kafin ya zama shugaban kasa, ana zargin Trump ba bukatar kasar Amurka ce ta saka shi halartar taron ba. Ana jita-jitar cewar bukatar kansa ce ta kai shi taron, musamman ganin cewar manyan masu kudi daga fadin duniya na halartar taron.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel