Nigerian news All categories All tags
Rubdugu! Duba wadanda suka alkawarin marawa Obasanjo baya don korar APC daga Aso Rock

Rubdugu! Duba wadanda suka alkawarin marawa Obasanjo baya don korar APC daga Aso Rock

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, yana tattara ‘yan siyasa domin hada karfi da karfe a cire shugaba Buhari daga ofis. Tsohon Shugaban ya nemi duk wadanda zasu goya masa dasu saka hannu akan shirin da ya tsara domin fitar da wannan gwamnati daga shugabancin kasar nan, domin ceto al’ummar kasar.

Rubdugu! Duba wadanda suka alkawarin marawa Obasanjo baya don korar APC daga Aso Rock

Rubdugu! Duba wadanda suka alkawarin marawa Obasanjo baya don korar APC daga Aso Rock

A ranar talatar nan ne Tsohon Shugaban kasar ya bawa kowa mamaki, inda ya bukaci shugaba Buhari da ya hakura da takara a zabe mai zuwa.

Inda ofis din shugaban kasa a ranar laraban nan, suka mai da mashi da martani da irin cigaban da ta kawo wa kasar nan.

DUBA WANNAN: Dan mari da ya share wata uku yana daure

Majiya mai karfi ta bayyana mana cewar, tsohon shugaban kasar ya cigaba da tattauna matsalolin da suke damun kasar tare da shugaba Buhari, amma ganin cewar kasar na cikin wani hali, shine ya saka shi ya fito fili ya bayyana wa al’umma.

Yace ya shiga damuwa sosai da har sai da ya dinga bin manyan ‘yan siyasar kasar nan akan neman mafita. Daga bisani ya yanke shawarar ya rubuta wasikar nan, wadda a yanxu, ta saka da yawa daga cikin jama’a suka fuskanci abinda yake faruwa. 

Da yake jawabi a jami’ar Oxford, tsohon Shugaban kasar ya yaba da kokarin da wasu shugabanin Afirka suke, na kokarin habaka tattalin arziki.

Da aka tambayeshi akan mai zai ce game da gwamnatin shugaba Buhari, sai yace lokaci bai yi ba da zai yi magana akan shi. Da dama daga cikin wadanda tsohon Shugaban kasar ya tuntuba, sun bashi goyon baya, inda suka ce lokaci yayi da ya kamata a nema wa kasar mafita.

Mista Obasanjon ya gudanar da tarurruka tare da tsofaffin shugabannin Najeriya, Sarakuna, ‘yan majalisar dokoki da sauran manya masu fada aji a kasar nan. 

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel