Mahara sun yi wa Otal kawanya suna ta kashe mutane a Kabul

Mahara sun yi wa Otal kawanya suna ta kashe mutane a Kabul

- Otal Intercontinental yana tara baki na kasashen waje

- Taliban kan so kashe Turawa domin sun hana ayi shari'ar Islama a kasar

- An ceto gommai daga cikin Otal din

Mahara sun yi wa Otal kawanya suna ta kashe mutane a Kabul

Mahara sun yi wa Otal kawanya suna ta kashe mutane a Kabul

Masu ta'addanci a kasar Afghanistan, watau Haqqani da Taliba da Al-qaida, da ma burbushin ISIL, ake zargi da kai hari a Otal din da Turawa ke shakatawa inda suke bi daki daki da harbi da sa wuta.

An dai ceto sama da mutum 150 kuma an kashe maharan da ke dauke da muggan bindigogi, amma sun kashe mutum biyar. Jami'an tsaro sunce sun shawo kan lamarin da la'asar din kasar, wanda daidai yake da sha biyu na rana a Najeriya.

DUBA WANNAN: Yar-Tsana don ssoyayya

Afghanistan dai yanzu tana karkashin tsarin dimokuradiyya, tsari da masu tsattsauran son addini ke gani ya haramta musulmi ya bi, sdai dai ayi sharia ta addini.

Wani jami'in ma'aikatar tsaro sun fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an fara binciken yadda maharan suka iya shiga otel din bayan da aka mika tsaron otel din ga wani kamfani mai zaman kansa mako biyu da suka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel