Zaben 2019: Zamu sayawa Buhari da Masari takardan takara – Matasan Daura

Zaben 2019: Zamu sayawa Buhari da Masari takardan takara – Matasan Daura

Kungiyar matasan masarautar Daura wato Daura Emirate Youth Progressive Movement (DEYPM), ta alanta niyyar sayarwa shugaba Muhammadu Buhari da gwamna Aminu Masari takardan sake takara a zaben 2019.

Shugaban kungiyar, Malam Abdulkadir Lawal, ya bayyana hakan ne a wani taron gangami da dubban matasan kananan hukumomi 5 da ke karkashen masarautar Daura suka halarta.

Kananan hukumomin sune Daura, Baure, Zango, Mai’adua da Sandamu.

Zaben 2019: Zamu sayawa Buhari da Masari takardan takara – Matasan Daura

Zaben 2019: Zamu sayawa Buhari da Masari takardan takara – Matasan Daura

Yace: “ Zamu sayi fom domin nuna goyon bayanmu ga shugabannin nan 2 don sake takara zabe.”

Gwamna Masari ya yi nasara wajen kawo sauyi bangaren ilimi, ayyuka, kiwon lafiya, cikin shekaru biyu kan karagar mulki,”.

KU KARANTA: Dubi hotunan amarya yayin da ta Haukace ana tsaka da shagalin bikinta, har ma yayyaga kayan amarcinta

Lawal ya kara da cewa Buhari dan aiken Allah ne saboda kafin zuwansa, al’umman arewa maso gabas na cikin halin ha’ula’I dalilin rikicin Boko Haram.

Kana ya yabi Buhari kan kokarin fadada tattalin arziki da kuma tarbiyyan ma’aikatan gwamnati.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel