2019: Nasarorin Buhari ya wuce na shekaru 16 na mulkin PDP – In ji Adebayo Shittu

2019: Nasarorin Buhari ya wuce na shekaru 16 na mulkin PDP – In ji Adebayo Shittu

- Nasarorin shugaba Buhari ya wuce na shekaru 16 na mulkin jam’iyyar PDP

- Ministan sadarwa ya ce ayyukan da shugaba Buhari da Osinbajo suka aiwatar sun isa 'yan Najeriya su sake zaben su

- Ministan ya ce shugaba Buhari ya taka rawar gani, saboda haka, ya cancanci karo na biyu a ofishin

Ministan harkokin sadarwa, Barista Adebayo Shittu, ya bayyana cewa, nasarorin da shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo suka samu, a cikin shekaru biyu da rabi na mulkin su, sun wuce nasarar da jam'iyyar PDP ta samu, a cikin shekaru goma sha shida .

Majiyar Legit.ng ta tabbatar cewa, ministan ya yi wannan magana a ranar Asabar, 20 ga watan Janairu a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a lokacin bikin kaddamar da ofishin yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari na yankin kudu maso yammacin kasar.

Ministan ya ce idan aka yi la’akari da ayyukan da shugaba Buhari da Osinbajo suka aiwatar a cikin shekaru biyu da suka gabata sun isa 'yan Najeriya su sake zaben su a shekara ta 2019.

2019: Nasarorin Buhari ya wuce na shekaru 16 na mulkin PDP – In ji Adebayo Shittu

Ministan harkokin sadarwa, Barista Adebayo Shittu

Shittu ya ce yana da tabbacin cewa nasarar da shugaba Buhari da Osinbajo suka samu a shekaru biyu da rabi yafi abin da mulkin PDP ta yi a shekaru 16.

KU KARANTA: 2019: An kaddamar da ofishin yakin neman zaben Buhari a Ibadan

Shittu ya ce shugaba Buhari ya taka rawar gani, saboda haka, ya cancanci karo na biyu a ofishin.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin taron sun hada da Isaac Adewole, ministan kiwon lafiya, Adebayo Shittu, ministan sadarwa, Ken Nnamani, tsohon shugaban majalisar dattijai kuma shugaban taro da Orji Uzor Kalu, tsohon gwamnan jihar Abiya da sauran manyan ‘yan jam’iyyar a yankin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel