Zaben 2019: Na ga Buhari a matsayin shugaban kasa, Atiku zai fadi - Fasto Ayodele

Zaben 2019: Na ga Buhari a matsayin shugaban kasa, Atiku zai fadi - Fasto Ayodele

- Fasto Elija Ayoldele ya ce babu dan takaran da zai iya ka da Buhari a zaben 2019

- Eilja ya shawarci tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ka da ya tsaya takara a zaben 2019 saboda zai fadi

Fasto Elija Ayoldele, Shugaban cocin lNRI Evangelical dake Oke Afa, Isolo, a jihar Legas, ya ce ya samu wahayi daga ubangiji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai lashe zaben 2019 idan jam’iyyar APC tsayar da shi takara.

A lokacin da yake jawabi akan sabuwar takarda da ya wallafa mai taken, “ Gargadi ga kasashen duniya” Ayodele ya ce, Buhari ne zai lashe zabe, amma ya gargadi shi akan rashin yin abubuwan yadda yakamata a kasar.

Faston ya gargadi tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, akan fitowa takaran shugaban kasa a 2019 saboda zai fadi.

Zaben 2019: Na ga Buhari a matsayin shugaban kasa, Atiku zai fadi - Fasto Ayodele

Zaben 2019: Na ga Buhari a matsayin shugaban kasa, Atiku zai fadi - Fasto Ayodele

Ya kuma shawarci gwaman jihar Ekiti, Ayodele Fayose, da kada ya kuskura ya tsaya takara shugaban kasar da za a gudanar a 2019.

KU KARANTA : Barayin sun kona wani yaro mai shekaru 12 a jihar Kogi

Ayodele yace, a wahayin da ya samu an nuna masa mulki zai tsaya a yankin Arewa. Buhari zai sha wahala a takaran da zai kara yi, amma shi zai ci zabe idan APC suka tsayar dashi.

“Ubangiji ya fada mun cewa babu dan takarar da zai iya kada shi, sai dai in bai tsaya takara ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel