Jihohi 16 sun shirya ba gwamantin tarayya hadin kai wajen kaddamar da shirin samar wa makiyaya filayen kiwo - Olukayode

Jihohi 16 sun shirya ba gwamantin tarayya hadin kai wajen kaddamar da shirin samar wa makiyaya filayen kiwo - Olukayode

- Jihohi 16 sun shirya samar wa makiyaya filayen

- Minitsan harkan noma ya ce shirin samar wa makiyaya filayen kiwo zai rage rikici tsakanin makiyaya da manoma a kasar

Jihohi 16 daga cikin jihohi 36 sun nuna ra’ayin ba gwmnatin tarayya hadin kai wajen kaddamar da kudirin ta na samar wa makiyaya filayen kiwo.

Bayan haka akwai wasu jihohi da ake sa ran za su ba gwamnatin hadin kai, inji hadimin ministan harkan noma, Dr. Olukayode Oyedele.

Amma jihar Taraba, Benuwe da Abia sunce gwamnatin tarayya ta cire su daga cikin kudirin ta na samar wa makiyaya filayen kiwo.

Jihohi 16 sun shirya ba gwamantin tarayya hadin kai wajen kaddamar da shirin samar wa makiyaya filayen kiwo - Olukayode

Jihohi 16 sun shirya ba gwamantin tarayya hadin kai wajen kaddamar da shirin samar wa makiyaya filayen kiwo - Olukayode

Audu Ogbe, ya sanar da masu ruwa da tsaki a kasar manufar gwamnatin tarayya akan samar wa makiyaya filayen kiwo a taruka da yayi da su.

KU KARANTA : Barayin sun kona wani yaro mai shekaru 12 a jihar Kogi

Ogbe yace gwamnatin zata samar wa makiyaya wuri daya da za su rika yin kiwo dabobin su, wurin da za su rika samu ruwan sha, da abinci.

Kuma za a samar musu asibitin dabbobi da kuma jami’an tsaron da za su kare dabobin daga barayin shanu.

Wannan kudiri yana daga ciki hanyoyin da gwamnatin tarayya ta ke so ta kawo karshen rikicin makiayya da manoma a kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel