Shugabannin kananan hukumomin jam'iyyar APC sun nemi Uba Sani ya tsaya takarar Sanata a Kaduna

Shugabannin kananan hukumomin jam'iyyar APC sun nemi Uba Sani ya tsaya takarar Sanata a Kaduna

- Shugabanin kananan hukumomi a Kaduna sun bukaci Malam Uba Sani ya fito takarar Sanata a zaben 2019

- Sun ce babu wanda ya fi dacewa ya wakilta jihar face shi domin jazircewar sa wajen aiki da gudunmawar da ya ke bayarwa ga al'ummar da ke jihar

- A halin yanzu dai, Kwamared Shehu Sani ne ke wakiltan yankin Kadunan ta tsakiya

Shugabannin kananan hukumomin shida dake karkashin sanatoriyar Kaduna ta tsakiya sun nemi mai bawa gwamna Nasiru El-Rufa'i shawara a kan harkokin siyasa, Malam Uba Sani, da fito takarar neman Sanata. Shugabannin sun bayyana haka ne bayan wani taro da suka gudanar ranar Juma'a, 19 ga watan Janairu, 2018.

A wata takarda da suka raba ga manema labarai a jiya Asabar, shugabannin kananan hukumomin sun bayyana cewar suna goyon bayan Malam Uba Sani ne saboda jazircewar sa da kuma irin gudunmawar da yake bayarwa ga jama'ar dake kananan hukumomin jihar Kaduna ta tsakiya.

new links

new links

"Malam Uba Sani ya samar da aiyuka sun fi dubu ga matasa a sabbin ma'aikatun gwamnatin jihar Kaduna da suka hada da KASTELEA, KADIPA, da sauran su. Kazalika ya bayar da tallafi ga matasa da dama," a cewar sanarwar.

Shugabannin sun kara da cewar, Malam Uba Sani, ba a iya jihar Kaduna kadai ya samarwa da aiyuka ba, ya samar da aiyuka ga matasa a gwamnatin tarayya karkashin tsarin NDE da kuma nemawa matasa jari a karkashin tsarin bunkasa harkokin noma na gwamnatin tarayya.

KU KARANTA: 'Yan a ware na PDP sunyi sulhu da uwar Jam'iyyar

"A bangaren kulawa da 'yan jam'iyya ba, ba'a barshi a baya ba, domin bai taba nuna gajiyawa ko kin sauraron bukatar 'yan jam'iyyar APC ba a Kaduna ta tsakiya," a cewar sanarwar da shugabannin suka raba.

Shugabannin sun ce wadannan halayen kirki da kuma nagartar da Malam Uba Sani keda ita ya saka su yanke shawarar mara masa baya domin ya kara samun damar cigaba da aiyuka ga mutanen yankinsa.

Wadanda suka saka hannu a kan takardar sanarwar sun hada da; Alhaji Musa Sheriff (Kaduna ta Arewa), Ibrahim Yakubu Soso (Kaduna ta Kudu), Injiniya Magaji Bala (Chikun), Bala Wakili (Kajuru), Abdullahi Jariri (Birnin Gwari), da Alhaji Ibrahim Musa (Giwa).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel