Barayin sun kona wani yaro mai shekaru 12 a jihar Kogi

Barayin sun kona wani yaro mai shekaru 12 a jihar Kogi

- Barayin waya sun kona wani karamin yaro a jihar Kogi saboda tsoron kada ya tona musu asiri

- Shugaban ma'aikatan gwaman jihar Kogi yayi alwkarin gwamnatin jihar Kogi zata gurfanar da barayin da suka kona karamin yaro a jihar

Barayi sun kona wani yaro mai sheakru 12, Ojonugwa, a karamar hukumar Ogugu, Olamaboro dake jihar Kogi a ranar Asabar.

Rahotonanni sun nuna cewa barayin sun kona yaron ne saboda tsoron kada ya tona musu asiri bayan sun sace wata wayar tarho da yaron yake da masaniya akai.

Barayin sun umarci yaron ya kwanata a kasa, ya rufe idanun sa, kafin suka banka mishi wuta.

Barayin sun kona wani yaro mai shekaru 12 a jihar Kogi

Barayin sun kona wani yaro mai shekaru 12 a jihar Kogi

Wani shaida mai tushe ya fadawa manema labaru cewa, barayin sun gudu akan babur din su yayin da yaron ya fara ihu yana neman taimako, wasu makwabta suka ruga cikin inda yake suka ceci rayuwan sa daganan suka garzaya dashi asibiti.

KU KARANTA : 2019: Bikin komawar tsohon gwamnan Kebbi da wasu 267,000 zuwa APC

Shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Kogi, Cif Edward Onoja, ya ziyarci yaron a Asibiti.

Cif Edward Onoja yayi alkwarin cewa gwamnati zata yi iya kokarin ta wajen ganin an kama barayin da suka aikata wannan mumunan laifi da gurfanar da su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel