Siyasar Kano: Akwai alamar za'a zub da jini a karshen watan nan

Siyasar Kano: Akwai alamar za'a zub da jini a karshen watan nan

- 30 ga watan Janairu ake sa rai za'a gamu, 'yan kwankwasiyya da na gandujiyya

- Kamar dai gwamnati ta tsakiya bata damu da me zai faru ba

- Samarin sun sha kashe kawunansu da zub da jinanen juna duk da cewa kabilarsu da addininsu da jiharsu da ma yarensu daya

Siyasar Kano: Akwai alamar za'a zub da jini a karshen watan nan

Siyasar Kano: Akwai alamar za'a zub da jini a karshen watan nan

Ga alama, samarin Kano basu dam da ransu ba domin 'yan siyasa da ke mulkar su. Domin kuwa, kamar yadda take ta faruwa a baya, ga alama za'a kuma kwatawa, domin kuwa, samarin suna nan suna wasa wukakensu domin saran juna.

Suna shiri ne domin a watan ranar 30 ga Janairun nan, uban tafiyar Kwankwasiyya zai zo gangami Kano, inda su ma masu son gwamna ya zarce, watau Gandujiyya 4+4, suke cewa ranar zasu fito jifar shaidan.

Siyasar Kano: Akwai alamar za'a zub da jini a karshen watan nan

Siyasar Kano: Akwai alamar za'a zub da jini a karshen watan nan

A baya ma dai, sau wajen karo uku, ana ssamun asarar rayuka, da dukiyoyi, da zub da jinin juna, dama na wadanda basu ji ba basu gani ba, akan irin wannan mummunar siyasa, kuma ya zuwa yanzu, babu wani dan manyan nan da ya leko aka yi rigimar iyayensa da shi, a kan talakka dai ta kare.

Sanata Kwankwaso dai da Gwamna Ganduje, kamar basu san me ke aruwa a kasa ba, ko kuma sun sani amma basu damu su dau matakin kare sake abkuwar hakan ba, ko ma kuma, su suke ingiza wutar a karkashin kasa.

DUBA WANNAN: Yar tsanar roba don saduwa ta kawo tarnaqi a al'umma

An jiyo dai Kwamishina guda sukutum, yana kira da a zo a tarbi gwamna murabus da duwatsu, kuma daga wannan kiran, an sami jikkata tun gamuwar bata zo ba.

Siyasar Kano dai ta saba da irin wadannan katobara da asarar rayuka, musamman lokutan zabe, ko na gwamna ko na kananan hukumomi. Kai har ma da na shugaban kasa.

Samarin dai, bassu jin kira, tunda sunyi shaye-shaye kafin su fito, ya rage ga masu hankali, ko suma zasu shiga ayi dasu, ko kuma hankali zayyi halinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel