Rikici dake tsakanin Ajimobi da Shittu zai iya janyo wa APC mastala a zaben 2019 – Orji Kalu

Rikici dake tsakanin Ajimobi da Shittu zai iya janyo wa APC mastala a zaben 2019 – Orji Kalu

- An kaddamar da Ofisihin nuna goyon bayan Buhari da Osinbajo a jihar Oyo

- Ministan sadarwa, Adebayo Shittu ya ce abubuwa da Buhari yayi a cikin shekaru biyu yafi abubuwan da PDP suka yi a cikin shekaru 16

Tsohon gwamnan jihar Abia, Dr. Orji Uzor Kalu yace rikicin dake tsakanin Gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi da Ministan sadarwa, Barista Adebayo Shittu zai iya janyo wa jam’iyyar APC cikas a zaben 2019.

Kalu ya bayyana haka ne a ranar Asabar a lokacin da ake kaddamar da ofishin nuna goyon bayan shugaban kasa Muhammmadu Buhari da mataimakin sa ferfesa Yemi Osinabjo na reshen Kudu maso yamma a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Ministan sadarwa, Adebayo Shittu ya gina ofishin wanda dake unguwar Mokola-Sango Road, dan fara yiwa Buhari kamfen din takarar shugaban kasa a 2019.

Rikici dake tsakanin Ajimobi da Shittu zai iya janyo wa APC mastala a zaben 2019 – Orji Kalu

Rikici dake tsakanin Ajimobi da Shittu zai iya janyo wa APC mastala a zaben 2019 – Orji Kalu

A cikin wadanda suka halarci taron akwai tsohon shugaban majalissar Dattawa, Sanata Ken Nnamani, Minitsan kiwon lafiya Ferfesa Isaac Adewole, da mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen Kudu maso yamma, Cif Pius Akinyelure.

KU KARANTA : Tarihi ya nuna asalin jihar Benuwe ta Fulani ce – Ferfesa Labo Muhammad

Kalu yace kaddamar da ofishin bai dame shi ba kamar yadda hadin kan mambobin jam’iyyar APC ya dame shi.

Adebayo Shitu a lokacin da yake jawabin a taron, ya ce Abubuwan da Buhari yayi a cikin shekaru biyu da suka gabata ya fi abubuwan da jam’iyyar PDP suka yi a cikin shekaru 16.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel