Rashin Imani: Ya sayar da yaron mutane kan N70,000

Rashin Imani: Ya sayar da yaron mutane kan N70,000

An kama wani shahararren mai garkuwa da mutane bayan ya sayar da wani yaron da ya sata kan naira dubu saba'in ga wasu mutanen da ya saba sayar wa yaran da yake satowa. Kimanin yara 40 aka ceto daga wurin wadanda yake sayarwa yaran.

Dubun wani shahararren mai garkuwa da mutane ta cika, inda aka cafke shi bayan ya sayar da wani yaron da ya sata kan naira dubu saba'in.

Wannan mutumin da ake zirgi da aikata wannan mumunar laifi, rahotanni sun bayyana cewa ya kammala karatun digiri.

An yi nasarar ceto yara kimanin 40 daga wurin wadanda ya sayarwa bayan ya yi garkuwa da su daya bayan daya.

Rashin Imani: Ya sayar da yaron mutane kan N70,000

Mai garkuwa da yaran mutane

Garkuwa da mutane a Najeriya a halin yanzu ta zama babban sana’a ga wasu marasa kishin kasar.

KU KARANTA: Ma'aikaciyar jinyan Asibiti ta hada baki da wata mata domin sayar da jariri

Idan dai baku manta a ranar Alhamis da ta gaba Legit.ng ta kawo muku cewa wasu ‘yan bindiga da ba a sani ba sun yi garkuwa da ‘yar Alhaji Salisu Mai-Tiles mai shekaru 14 da haihuwa a yankin karamar hukumar Kankia da ke jihar Katsina.

Daga bisani kuma suka bukaci miliyan dari daga mahaifin yarinya a matsayin kudin fansa.

Hakazalika, a ranar Asabar da ta gabata kuma jami’an tsaro suka kubutar da wasu ‘yan kasashen waje huku a hannun wadanda suka sace su a Kaduna.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel