Mamba a majalisar wakilai ta kasa ta gano abinda ke saka 'yan Najeriya rashin hakuri

Mamba a majalisar wakilai ta kasa ta gano abinda ke saka 'yan Najeriya rashin hakuri

- 'Yar majalisar wakilai, Aishatu Dukku, ta ce yawan shan Maggi ke saka 'yan Najeriya rashin hakuri

- Ta ce Allah ya halicci makiyaya da kaunar shanu fiye da rayuwar su

- Dan majalisa, Hassan Saleh, ya mayar mata da raddi

Tsohuwar minista kuma mamba a majalisar wakilai ta kasa daga jihar Gombe, Aishatu Dukku, ta zargi shan Maggi da zama dalilin rashin hakurin 'yan Najeriya.

Aishatu ta bayyana hakan ne yayin da majalisar ta wakilai ke tafka mahawara a kan rikicin makiyaya da manoma da ya addabi jihar Benuwe.

Mamba a majalisar wakilai ta kasa ta gano abinda ke saka 'yan Najeriya rashin hakuri

Mamba a majalisar wakilai, Aishatu Dukku

A cewar Aishatu " 'Yan Najeriya basu da hakuri, basa son taimakon juna, basa son warware matsalolin dake damunsu watakila saboda yawan shan Maggi ne ya saka bamu da hakuri."

DUBA WANNAN: Majalisar dattijai za ta gudanar da muhimmin taro na kwanaki biyu a sati ma zuwa

Aishatu ta cigaba da cewar "Makiyaya suna da kaunar shanunsu fiye da mutane, sun ma fi kaunar shanunsu da kansu, haka Allah ya halicce su."

Saidai wadannan kalamai na 'yar majalisa Aishatu Dukku bai yi wa honarabul Hassan Saleh, dan majalisar daga jihar Benuwe, dadi ba, domin kuwa ya mayar mata da raddi.

"Ban yarda cewar haka Allah ya halicci makiyaya ba, shanu biliyan goma basu da darajar koda ran mutum guda. Tamkar cin fuska ne wani ya yi kokarin kare makiyayan ta hanyar yin irin wadannan furuci," inji honarabul Saleh.

Aishatu Dukku mamba ce a majalisar wakilai daga jihar Gombe kuma tsohuwar ministar ilimi lokacin mulkin Jonathan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel