Shehu Sani ya jinjina wa jami’an tsaro bisa kubutar da turawa huɗu da aka sace a Kaduna

Shehu Sani ya jinjina wa jami’an tsaro bisa kubutar da turawa huɗu da aka sace a Kaduna

- Sanata Shehu Sani ya yaba wa jami’an tsaro bisa ceto turawa huɗu da aka yi garkuwa da su a Kaduna

- Sani ya ce Sufeto Janar na ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun taka rawar gani.

- Sanatan ya lura cewa akwai bukatar magance matsalolin sace-sacen mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Sanata Shehu Sani mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya ya yaba kokarin jami’an ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro a kasar bisa ceto wasu turawa ‘yan kasashen waje da aka yi garkuwa da su a Kaduna.

Legit.ng ta tattaro cewa, sanatan ya ce Sufeto Janar na ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun taka rawar gani.

Amma, sanatan ya lura cewa akwai bukatar magance matsalolin sace-sacen mutane a kan hanyar da ta hada Kaduna, Abuja da kuma Neja yayin da aka samu labarin cewa a sake sace wasu mutane a hanyar.

Shehu Sani ya jinjina wa jami’an tsaro bisa kubutar da turawa huɗu da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Sanata Shehu Sani mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya

Idan dai baku manta ba a safiyar ranar Asabar da ta gabata ne hukumar ‘yan sanda ta sanar cewa ta ceto turawa hudu ‘yan kasashen Amurka da Canada da wasu ‘yan bindiga suka sace a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

KU KARANTA: An ceto turawa huɗu da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Tuni aka miƙa turawan ga cibiyar jakadancin ƙasar Amurka da ke birnin Abuja domin duban lafiyarsu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel