2019: Bikin komawar tsohon gwamnan Kebbi da wasu 267,000 zuwa APC

2019: Bikin komawar tsohon gwamnan Kebbi da wasu 267,000 zuwa APC

Jam'iyya mai mulki ta APC reshen jihar Kebbi ta gudanar da bikin karbar tsohon gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Usman Nasamu Dakingari, da tare da wasu ‘ya’yan jam’iyyar PDP 267,000 zuwa APC a birnin Kebbi. An gudanar da taron a birnin Kebbi a ranar Asabar.

Jam'iyya mai mulki ta APC reshen jihar Kebbi ta karbi tsohon gwamnan jihar, Alhaji Usman Nasamu Dakingari da mataimakinsa da kuma wasu 'yan jam'iyyar PDP 267,000 wadanda suka yi watsi da jam'iyyar a watan jiya.

A ranar Asabar, 20 ga watan Janairu ne aka gudanar da bikin karbar manyan 'yan jam'iyyar PDP da suka dawo APC a karkashin jagoracin tsohon gwamnan.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari , an gudanar da bikin ne a filin kwallo na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi, babbab birnin jihar wanda gwamnan jihar Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya jagoranci bikin karbar magoya bayan na PDP zuwa APC.

2019: Bikin komawar tsohon gwamnan Kebbi da wasu 267,000 zuwa APC

Tsohon gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Usman Nasamu Dakingari da wasu manyan 'yan siyasa da suka canza sheka zuwa APC

Dakingari wanda ya jagoranci jihar na tsawon shekaru takwas a karkashin PDP ya canza sheka zuwa APC a bikin liyafar da aka shirya masa da wasu tsoffin shugabannin PDP wadanda suka koma APC.

2019: Bikin komawar tsohon gwamnan Kebbi da wasu 267,000 zuwa APC

Bikin komawar tsohon gwamnan Kebbi da wasu 267,000 zuwa APC

KU KARANTA: 2019: An kaddamar da ofishin yakin neman zaben Buhari a Ibadan

Da yake jawabi a lokacin bikin, shugaban APC a jihar Kebbi, Barista Attahiru Maccido ya ce shawarar sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki da tsoffofin ‘ya’yan babban jam’iyyar adawa ta PDP suka yi ya biyo bayan kyakyawar shugabancin Muhammadu Buhari da gwamna Abubakar Atiku Bagudu a jihar Kebbi.

Shugaban ya ce za a yi wa wadanda suka canza shekar adalci da sauran tsoffin mambobin jam’iyyar.

Amma duk da haka ya umarce su su yi ƙoƙari su bi kundin tsarin mulki da kuma dokokin jam’iyyar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel