2019: An kaddamar da ofishin yakin neman zaben Buhari a Ibadan

2019: An kaddamar da ofishin yakin neman zaben Buhari a Ibadan

- An kaddamar da ofishin yakin neman zaben shugaba Buhari a Ibadan

- Gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, ya kaurace ma taron

- An nada ministan sufuri a matsayin babban darekta na tawagar yaƙin neman zaben shugaba Buhari

Jiga-jigan jam’iyya mai mulki ta APC a yankin kudancin kasar sun hadu a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Asabar, 20 ga watan Janairu don kaddamar da ofishin yakin neman zaben Buhari da Osinbajo.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin taron sun hada da Isaac Adewole, ministan kiwon lafiya, Adebayo Shittu, ministan sadarwa, Ken Nnamani, tsohon shugaban majalisar dattijai da kuma Orji Uzor Kalu, tsohon gwamnan jihar Abiya.

Duk da haka, Abiola Ajimobi, gwamnan jihar, ya nisanci kansa daga taron.

2019: An kaddamar da ofishin yakin neman zaben Buhari a Ibadan

Jiga-jigan jam’iyya mai mulki ta APC a yankin kudancin Najeriya

Legit.ng ta tattaro cewa, an gudanar da wannan bikin ne kwana daya bayan Rochas Okorocha, gwamnan jihar Imo, ya ce dukkannin gwamnonin APC sun amince shugaba Buhari ya zarce a 2019.

KU KARANTA: Mafi kyawun buri a rayuwata shine yiwa Najeriya da shugaba Buhari hidima - Ahmed Rufa'i Abubakar

Okorocha ya ce an nada Rotimi Amaechi, ministan sufuri, a matsayin babban darekta na tawagar yaƙin neman zaben shugaba Buhari.

Har yanzu shugaba Buhari bai bayyana ra'ayinsa ba game da zaben 2019, ko da yake yana tattauna tare da shugabannin jam'iyyarsa da magoya bayansa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel