Kasar Zimbabwe ta sake fadawa cikin dambarwar siyasa

Kasar Zimbabwe ta sake fadawa cikin dambarwar siyasa

Jam'iyyar siyasa dake mulki a kasar Zimbabwe ta ZANU -PF na neman sake fadawa cikin wata sabuwar dambarwa bayan da ta kori akalla mutane sha daya daga rike da madafun iko cikin su kuwa hadda 'yan majalisun da ke da kusanci da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe.

Wannan dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu na zuwa ne yayin da sabon shugaban kasar mai suna Emmerson Mnangagwa ke cigaba da tankade da rauraya a gwamnatin sa tare da fitar da dukkan sauran tsirarun magoya bayan tsohon shugaban kasar Mugabe da kuma matar sa.

Kasar Zimbabwe ta sake fadawa cikin dambarwar siyasa

Kasar Zimbabwe ta sake fadawa cikin dambarwar siyasa

Legit.ng dai ta samu cewa a cikin watan Nuwambar bara ne kasar ta Zimbabwe ta afka cikin yanayin rashin tabbas kafin daga bisani a hambarar da shugaban kasar na wancen lokacin tare kuma da maye gurbin sa da mataimakin sa.

A wani labarin kuma, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) a turance watau Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa kawo yanzu akalla mutane 'yan Najeriya miliyan 74 ne suka yanki katin zabe.

Babban daraka a hukumar dake da kula da sha'anin wayar wa da al'umma kai game da zaben tare da kuma mai magana da yawun hukumar Oluwole Osaze-Uzzi shine ya bayyana hakan jiya Juma'a a garin Abuja.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel