'Yan a ware na PDP sunyi sulhu da uwar Jam'iyyar

'Yan a ware na PDP sunyi sulhu da uwar Jam'iyyar

- Wasu yan jam'iyyar PDP ta suka ware kansu bisa rashin amincewa da sakamakon zaben Ciyaman Uche Secundus sun mayar da takuban su

- 'Yan a ware din da akafi sani da 'FRESH PDP' sun ce sunyi sulhun ne domin cigaba najeriya da fuskantar zabe mai zuwa a 2019

- Jagoran yan a ware din, Olukayode Akindele ne ya sanar wa manema labari sun hade kansu da uwar jam'iyyar bayan sunyi wata ganawa da sukayi da tsohon Ciyaman din jam'iyyar, Okwesilieze Nwodo

Wasu yan a ware daga Jam'iyyar PDP da suke kiran kansu da 'Fresh PDP' sunyi sulhu kuma hade the uwar Jam'iyyar. Dama yan a waren sunyi tawaye ne sakamakon zaben shugabancin Jam'iyyar da aka yi a ranar 9 ga watan Disambar 2017 da Uche Secundus ya lashe zaben.

A yayin da yake bayar da sanarwan sulhun bayan sun gana da tsohon Ciyaman na jam'iyyar, Okwesilieze Nwodo a ranar Asabar a Abuja, shugaban yan a waren, Olukayode Akindele, ya ce lokaci ya yi da su tsagaita wuta.

'Yan a ware na PDP sunyi sulhu da uwar Jami'iyyar

'Yan a ware na PDP sunyi sulhu da uwar Jami'iyyar

DUBA WANNAN: Wani Likita ya kamu da Zazzabin Lassa a Jihar Kogi

A jawabin da ya yi wa manema labarai bayan taron da sukayi da tsohon Ciyaman din jam'iyyar ta PDP, Akindele ya ce sun mayar da takuban su ne sun rungumi sulhu domin cigaban Najeriya da kuma babban zabe mai zuwa a 2019.

Akindele kuma ya mika jerin sunayen mutanen da ya kira mambobin kwamitin gudanarwa na asali.

A gefe guda kuma, Nwodo ya ce anyi sulhun ne da sanin yan kwamitin amintattun na jam'iyyar har ma da sanin yan kwamitin gudanarwa da ma sauran rassan Jam'iyyar.

"Mun gane kurakuren mu kuma yanzu a shirye muke mu dawo domin daura kasar nan kan turba na cigaba" inji Nwodo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel