Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawarar

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawarar

- Buhari da kansa ya kafa kwamiti domin samo sabon shugaban NIA

- NIA ita ce hukumar leken asiri a wajen Najeriya

- An sauke wanda ke shugabantar hukumar bayan da aka kama kudi a hannun matarsa

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawarar

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawarar

Sabon shugaban hukumar leken asiri ta NIA, watau wanda shugaba Buhari ya nada, bayan da ya sauke mista Oke, ya fara aiki a hukumar a makon nan.

Sai dai nadin sa ya zo wa wasu kabilun da haushi, musamman daga kudancin Najeriya, bayan da suke ganin an hausantar da abin ga 'yan arewa, komai na tsaro ana baiwa musulmi.

Kokensu ya kai ga kunnen shugaban, sai dai bai tanka musu ba, amma yayi hannunka mai sanda a dinar da ya hada a fadarsa a daren Laraba, inda ya gaya wa jam'iyyarsa dalilansa na daukar wasu matakai musamman na tsaro.

DUBA WANNAN: Soyayyar saduwa da 'yar-tsana, ko yaya abin yake?

A yanzu dai, sai ga sabon bincike jaridar Premium Times ta fitar, wanda ya leka rahoton da kwamitin bin bahasin lamarin NIA din tun bayan badakalar kudaden da aka kama a Legas karkashin matar shugaban hukumar tana aikin boye su.

Rahoton, wanda Babagana Kingibe ya gudanar, ya nuuna cewa ba wannan shugaban na yanzu da Buhari ya nada suka ce ya nada ba, hasali ma, shugaban kwata-kwata bayyi aiki da rahoton ba.

A cikin ma'aikatan hukumar, watau daraktoci kwamitin ya ce shugaban ya zabo wanda zai shugabanci hukumar, amma sai ya zabo Mista Abubakar, wanda ya dade da yin ritaya daga hukumar, kuma bai kai wani matsayi ko yayi wani aikin kuzo-ku-gani ba a hukumar, hasali ma, ba a Najeriya aka haife shi ba, ba kuma a nan ya girma ba, a Chadi yayi wayau.

Rahoton ya kuma nuna yadda Mista Abubakar ya gagara cin jarrabawa da aka yi ta yi masa ta karin matsayi, don haka ma ne yayi ritaya baki daya daga aikin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel