An sa ladar Naira 10 miliyan ga duk wanda ya gulmata wadanda suka kashe dan majalisar Taraba

An sa ladar Naira 10 miliyan ga duk wanda ya gulmata wadanda suka kashe dan majalisar Taraba

Jami'an rundunar hukumar 'yan sandan kasar Najeriya shiyyar jihar Taraba ta sanar da ladar makudan kudin da suka kai Naira 10 miliyan ga duk wanda ya bayyana masu wani bayanin da zai taimaka wajen damke bata-garin da suka kashe dan majalisar Taraba, Mista Hosea Ibi.

Kwamishinan 'yan sandan jihari mai suna Mista Dave Akinremi shine ya sanar da hakan a yayin da yake zantawa da manema labarai jiya Juma'a a garin Jalingo babban birnin jihar.

An sa ladar Naira 10 miliyan ga duk wanda ya gulmata wadanda suka kashe dan majalisar Taraba

An sa ladar Naira 10 miliyan ga duk wanda ya gulmata wadanda suka kashe dan majalisar Taraba

Legit.ng dai ta samu cewa haka zalika kwamishin 'yan sandan ya kuma bayar da tabbacin cewa tuni hukumar rundunar ta kara kaimi wajen ganin ta gano wadanda suka kashe shi din.

A wani labarin kuma, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) a turance watau Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa kawo yanzu akalla mutane 'yan Najeriya miliyan 74 ne suka yanki katin zabe.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel