Gwamnonin jam'iyyar APC sun amince da tazarcen shugaba Buhari

Gwamnonin jam'iyyar APC sun amince da tazarcen shugaba Buhari

Shugaban gamayyar gwamnonin jihohin Najeriya a karkashin jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Imo dake a kudu maso gabashin Najeriya mai suna Mista Rochas Okorocha ya bayyana sanarwar cewa dukkan ilahirin 'ya'yan kungiyar ta su sun amince da tazarcen shugaba Buhari a zaben 2019.

Gwamnan na Imo ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a babban filin sauka da tashin jirage dake a garin Owerri babban birnin jihar ta Imo.

Gwamnonin jam'iyyar APC sun amince da tazarcen shugaba Buhari

Gwamnonin jam'iyyar APC sun amince da tazarcen shugaba Buhari

Legit.ng ta samu cewa haka zalika Gwamnan ya kara da cewa gwamnonin sun cimma wannan matsayar ne bayan da sun yi duba na tsanaki ga yadda yake gudanar da mulkin kasar tare da kokarin dora kasar akan turbar da ta dace.

Haka zalika ya bayyana cewa gwamnonin sun sake amincewa da nadin Ministan sufuri sannan kuma tsohon gwamnan jihar Ribas a matsayin wanda zai jagoranci kamfe din yakin neman zaben shugaban kasar a 2019.

A wani labarin kuma, mun samu cewa Uwar gidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari a wani salo na dubara ta sake caccakar salon mulkin mai gidan ta, shugaba Muhammadu Buhari a jiya bayan da ta sake yada kalaman adawa da suka na wasu Sanatoci da sukayi ga mijin nata a kafar sadarwar zamanin ta na Tuwita.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel