Gwamnatin Buhari na shirin ciwo bashin cikin gida na Naira 385 biliyan

Gwamnatin Buhari na shirin ciwo bashin cikin gida na Naira 385 biliyan

Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin ciwo wani sabon bashin da zai kai akalla Naira 315 biliyan zuwa Naira 385 biliyan daga cikin gida a cikin kason farko na wannan shekarar ta 2018.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da hukumar dake kula da harkokin bashi ta gwamnatin tarayyar ta fitar a karshen makon jiya, ranar juma'a kamar dai yadda majiyar mu ta ruwaito mana.

Gwamnatin Buhari na shirin ciwo bashin cikin gida na Naira 385 biliyan

Gwamnatin Buhari na shirin ciwo bashin cikin gida na Naira 385 biliyan

Legit.ng dai ta samu haka zalika daga cikin takardar cewa gwamnatin zata yi anfani da bashin ne wajen samar wa da al'ummar kasar kayayyakin more rayuwa.

A wani labarin kuma, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) a turance watau Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa kawo yanzu akalla mutane 'yan Najeriya miliyan 74 ne suka yanki katin zabe.

Babban daraka a hukumar dake da kula da sha'anin wayar wa da al'umma kai game da zaben tare da kuma mai magana da yawun hukumar Oluwole Osaze-Uzzi shine ya bayyana hakan jiya Juma'a a garin Abuja.

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel