Wani Likita ya kamu da Zazzabin Lassa a Jihar Kogi

Wani Likita ya kamu da Zazzabin Lassa a Jihar Kogi

- Wani likita ma'aikacin Cibiyar Kiwon Lafiya ta Gwamnatin Tarayya na Jihar Kogi ya kamu da zazzabin Lassa

- Daraktan Cibiyar na Jihar, Dakta Olatunde Alabi, shi ne ya tabbatarwa manema labarai da hakan a ranar Asabar

- Jihar tare da Kungiyoyi da Ma'aikatun Kiwon Lafiya sun dukuta wurin samar da magani da kuma hana yaduwar cutar

Jihar Kogi ta tabbatar da kamuwa da zazzabin lassa da wani likita ya yi, mai aiki a Cibiyar Kiwon lafiya na Gwamnatin Tarayya na Lokoja a Jihar. Daraktan Cibiyar, Dakta Olatunde Alabi, shi ne ya shaidawa manema labari a ranar Asabar.

Alabi ya bayyana cewan likitan mai shekaru 30 ya kamu da cutar ne a ranar 19 ga watan Janairu. An gwada jinin sa a Cibiyar Kiwon Lafiyar da ke Irrua, Jihar Enugu, inda a can ne a ka tabbatar da jinin na dauke da kwayar cutar.

Wani Likita ya kamu da Zazzabin Lassa a Jihar Kogi

Wani Likita ya kamu da Zazzabin Lassa a Jihar Kogi

KU KARANTA: Za'a fara gina filayen kiwon Shanu cikin mako mai zuwa - Gwamnatin Tarayyah

Sakamakon haka ne a ka garzaya da shi can Cibiyar ta Irrua don samun magani da cikakken kulawa. Tuni kuma a ka fara binciken mutanen da ya yi mu'amala da su a gida ko wurin aiki don hana yaduwar cutar.

Daraktan ya kuma bayyana cewar Kungiyar Kiwon Lafiya na Duniya da kuma Ma'aikatar Kiwon Lafiya na Jihar da sauran ma su fada a ji a lamarin, su na iya kokarin su ga Jihar dangane da cutar. Ita kuma Jihar ta dukufa da wayar wa jama'a da kai game da kamuwa da kuma yaduwar cutar don a kiyayewa.

Cibiyar ta yi kira ga al'umma da su guji barin hatsi da sauran nau'ukan abinci a bude. Bugu da kari, a tabbata an kori beraye da su ke haifar da cutar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel