An ceto turawa huɗu da aka yi garkuwa da su a Kaduna

An ceto turawa huɗu da aka yi garkuwa da su a Kaduna

'Yan ƙasashen Amurka da Canada huɗu da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna sun samu 'yanci.

Wani babban jami'in ɗan sanda ne ya bayyana hakan da cewar, an ceto su ne da misalin ƙarfe 7:30 na safiyar yau asabar cikin hali na buƙatar kulawa, inda aka miƙa su cibiyar jakadancin ƙasar Amurka dake birnin Abuja domin duban lafiyarsu.

Rahotanni da sanadin jaridar The Punch sun bayyana cewa, mutane biyu da ake zargi da aikata laifin sun shiga hannu a sakamakon jarumtar ƙungiyar rundunar 'yan sanda ta jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin sufeto janar na 'yan sanda.

An sako turawa hudu da aka yi garkuwa da su a Kaduna

An sako turawa hudu da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Waɗannan turawan da aka ceto sun haɗar da; Nate Vangeer ɗan ƙasar Canada, John Kirlin da kuma Dean Slocum 'yan ƙasar Amurka, sai kuma wata mata Rachael Kelly, ta ƙasar Canada.

KARANTA KUMA: Dole sai gwamnati ta yi la'akari da fushin kowace ƙabila - Inji Obasanjo

Legit.ng ta fahimci cewa, masu garkuwar sun yi gaba da waɗannan turawa ne a kan hanyar Kwoi-Jere dake ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna tun a ranar talatar da ta gabata.

A yayin ziyarar aiki da turawan suka kai garin Kafanchan na ƙaramar hukumar Jama'a, 'yan ta'adda suka buɗe musu wuta, inda rayukan jami'ai biyu suka salwanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel