Da gaske ake fada da rashin gaskiya yanzu a Najeriya – NSA Munguno

Da gaske ake fada da rashin gaskiya yanzu a Najeriya – NSA Munguno

- Shugaban EFCC yace babu gudu babu ja da baya wajen yaki da barna

- A makon nan Hukumar ta EFcc ta yaye sababbin Jami’an ta a Kaduna

- Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro yayi jawabi a taron

Mun samu labari cewa an yaye wasu sababbin Jami’an Hukumar EFCC a Najeriya. A wajen taron Hadimin Shugaban Kasa Buhari ya bayyana cewa da gaske ake yaki da rashin gaskiya yanzu a Kasar.

Da gaske ake fada da rashin gaskiya yanzu a Najeriya – NSA Munguno

Hukumar ta EFCC ta yaye sababbin Jami’an ta a Kaduna

Mai ba Shugaba Buhari shawara kan harkokin tsaro watau Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya ya bayyana cewa yanzu ba da wasa ake kokarin yaki da rashin gaskiya a kasar ba. Janar Munguno kuma yace ya zama dole a samu nasara.

KU KARANTA: Abin da ya hana Shugaba Buhari gayyatar Tinubu zuwa taro

Da gaske ake fada da rashin gaskiya yanzu a Najeriya – NSA Munguno

Munguno yace da gaske Shugaba Buhari ke fada da barna

Munguno ya bayyana wannan ne a wajen taron yaye sababbin Jami’an Hukumar EFCC a Makarantar NDA ta Sojojin Najeriya a Kaduna a makon nan. Mai ma Shugaba Buhari shawara yace wannan Gwamnatin ba ta dauki abin da wasa ba.

Shugaban Hukumar na EFCC watau Ibrahim Magu ya gana da manema labarai bayan taron inda ya tabbatar da cewa babu gudu babu ja da baya wajen shirin sa na yaki da barna a Kasar. Magu yana sa ran za su gama da duk binciken da ke gaban su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel