Dalilin da yasa bana so a kiraye ni da sunan 'Dakta Olusegun Obasanjo'

Dalilin da yasa bana so a kiraye ni da sunan 'Dakta Olusegun Obasanjo'

A yau ne asabar jami'ar NOUN (National Open University of Nigeria) zata gudanar da bikin yaye dalibai, inda zata karrama tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da shaidar kammala karatun digiri na uku a fannin nazarin addinin kirista.

Shugaban jami'ar, Farfesa Abdallah Adamu ya bayyana cewa, tsohon shugaban kasar yana ɗaya daga cikin ɗalibai 14, 771 da jami'ar zata karrama a bikin yaye ɗalibai karo na 17 da za a gudanar a Abuja, ya kuma kasance ɗalibi na farko da ya kammala karatun digiri na uku a jami'ar.

A yayin ganawa da 'yan jaridar Premium Times a safiyar yau asabar, dangane da ko zai yi sha'awar a kiraye shi da sunan 'Dakta Obasanjo' a sakamakon wannan munzali da ya taka a fagen karatu, tsohon shugaban yace sam baya bukatar hakan.

Cif Olusegun Obasanjo

Cif Olusegun Obasanjo

Yake cewa, ya fi bukatar a ci gaba da kiranshi Cif Obasanjo, domin shine karamcin da ya karɓa a yayin da hau shugabancin kasar nan tun a shekarar 1999 bayan ya watsar da karamcin 'Janar' kasancewarsa zaɓaɓɓen shugaba na dimokuraɗiya.

KARANTA KUMA: Ina da yaƙinin Buhari zai haɓaka tattalin arzikin Najeriya - Oshiomhole

Da yake bayyanawa manema labarai dalilin ra'ayinsa, tsohon shugaban ya bayyana cewa, hakan zai janyo rikicewa a tsakanin al'umma wajen banbancewa, kasancewar babban ɗan sa, 'Dakta Olusegun Obasanjo' yana amfani da wannan sunan bayan ya kammala digiri ɗinsa na uku a fannin nazarin zanen gine-gine, saboda haka ya zaɓi 'Cif Olusegun Obasanjo'.

A kalamansa cikin raha, "ɗan da na haifa bashi da karamcin 'Cif', saboda haka a wannan fanni ina gaba dashi. Duk wanda yace 'Cif Olusegun Obasanjo' babu tantama ni yake nufi ba ɗa na ba."

Shugaban jami'ar, Farfesa Adamu ya kara da cewa, babu shakka Obasanjo ya ladabtar da kansa duk da kasancewar sa tsohon shugaban kasa wajen cancantar karamcin da ya samu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel