Adadin yaran Najeriya marasa zuwa makaranta ya ragu zuwa 8.6% - Ministan Ilimi

Adadin yaran Najeriya marasa zuwa makaranta ya ragu zuwa 8.6% - Ministan Ilimi

- Adadin ya ragu ne da kashi 1.9 cikin dari kasancewar ya sauka daga 10.5 zuwa 8.6

- Ministan Ilimi, Adamu Adamu, shi ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a

- Ministan ya yi kira ga 'yan siyasa da su bayar da na su gudummuwar don ilmantar da yara a yankunan su

A ranar Juma'a ne Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana cewar adadin yara marasa zuwa makaranta ya sauka da 1.9% , ya sauka ne daga 10.5% zuwa 8.6%. Adamu ya alakanta wannan cigaba a kokarin da shugaban Kasa Buhari ke yi da kuma tsarin ciyarwa a makarantu da a ka farar.

Ya yi bayyana hakan ne ga Magatakardan Hukumar Tantance Malamai na Kasa, Farfesa Ajiboye Josiah, a yayin bukin kaddamar da Fafutukar Shigar da Yara a Makarantu na Kasa da a ka yi a Makarantar Firamare na Tudun Salmanu da ke Bauchi.

Adadin yaran Najeriya marasa zuwa makaranta ya ragu da 8.6% - Minista

Adadin yaran Najeriya marasa zuwa makaranta ya ragu da 8.6% - Minista

DUBA WANNAN: Matsin lambar da ake wa iyalan Jonathan ya isa haka: MASSOB ga Gwamnatin Tarayya

Adamu ya bayyana wannan Fafutukar da kuma tsarin karatun Tsangaya ta Makarantun Al-Qur'ani da a ka riga a ka fara, a matsayin hanyar rage yara masu gararanba kan titi zuwa cikin aji don karatu.

Daga 2015, an kuma fara samawar makarantu guda 7875 da kujeru da kayakin cikin aji a kowace shekara, har na tsawon shekaru 4. Wannan duk a yunkurin Gwamnatin Buhari ne na kula da yara 'yan makaranta guda 2,725,000. Za kuma a rinka daukan sabbin kwararrun malmai don bayar da cikakkiyar kulawa ga daliban.

Ma'aikatar na sa ta kuma samu kyakkyawar fahimta da Hukumar Bautar Kasa ta NYSC na game da bayar da nata gudummuwar. Ministan ya kuma yi kira ga 'yan siyasa da su yi koyi da irin wannan fafutuka don bayar da na su gudummuwar a yankunan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel