Dole ne Gwamnati ta mayar da hankali kan warware matsalolin kabilanci a Najeriya - Obasanjo

Dole ne Gwamnati ta mayar da hankali kan warware matsalolin kabilanci a Najeriya - Obasanjo

- Tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kasance mai sauraron koke-koken dukan al'umma

- Tsohon shugaban ya bayar da wannan shawarar ne a bikin ya ye dalibai na Jami'ar NOUN da ke Abuja

- Shugaban Jami'an, Farfesa Abdallah Adamu kamalla digiri na 3 da Obasanjo ya yi abin nuni da cewa gemu baya hana neman ilimi

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce dole ne gwamnati ta saurari koke-koken al'umma daga dukan sassan kasar nan. Ya ce hakan ne kawai za sai kowane kabila ta samu natsuwa kan cewa ana dama wa da ita.

Obasanjo ya bayar da wannan shawar ne a rannan Juma'a wajen taron yaye dalibai na 'National Open Univerisity' a babban birnin Tarayyah, Abuja.

Ya zama dole Gwamnati ta warware matsalolin kabilanci, inji Obasanjo

Ya zama dole Gwamnati ta warware matsalolin kabilanci, inji Obasanjo
Source: Twitter

Tsohon shugaban kasan ya ce taron tattaunawa kan yiwa kas garambawul za baiwa dukkan al'umma daman su fadi ra'ayoyin su kan abubuwan da ke damun su kuma watakila su bayar da shawarwarin yadda za'a shawo kan al'amamuran.

KU KARANTA: Ma'aikaciyar jinyan Asibiti ta hada baki da wata mata domin sayar da jariri

Duk dai a wajen taron bikin yaye daliban, Shugaban Jami'ar Igbinedion da ke jihar Edo, Farfesa Eghosa Osaghe ya gabatar da wata lakcha mai taken 'Garambawul da tsarin mulkin raba dai-dai' wanda tayi karin haske kan al'amuran da ke fuskantar kasar nan a yanzu.

Osagie ya ce irin tsarin gwamnatin Najeriya za ta dore ne kawai idan an rungumi tsarin mulkin raba dai-dai ingantaciya.

A jawabin sa, Shugaban Jami'ar ta NOUN, Farfesa Abdalla Adamu ya ce darasi ne sosai yaddatsohon shugaban kasan, Obasanjo, ya dawo makaranta kuma ya kamalla karatun digiri din sa na 3, hakan ya nuna cewa gemu baya hanna neman ilimi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel