Matsin lambar da ake wa iyalan Jonathan ya isa haka: MASSOB ga Gwamnatin Tarayya

Matsin lambar da ake wa iyalan Jonathan ya isa haka: MASSOB ga Gwamnatin Tarayya

- Shugaban Kungiyar, Uchenna Madu, shi ne ya yi wannan jawabi a ranar Juma'a

- Ya ce tozarcin da Patience ke fuskanta ba komai ba ne illa nuna kiyayya ga 'yan kabilar Igbo

- Don haka ne ya yi kira ga 'yan kabilar da su cire tsoro su tashi tsaye don kare 'yan uwan su

Kungiyar Fafutukar Tabbatar da Kasar Biyafara wato MASSOB, ta ce da Gwamnatin Tarayya ta daina cin mutumcin iyalan Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, musamman matar sa Patience. Kungiyar ta yi wannan jawabi ne a ranar Juma'a ta bakin Shugaban ta Uchenna Madu.

Madu ya ce, ba komai Jonathan ke fuskanta ba illa lalube cikin duhun wannan Gwamnatin a kokarin ta na zubar ma sa da mutumci. Ya kuma ce Gwamnatin ta na son disashe hasken tauraruwar Patience ne saboda irin goyon bayan da ta ke yi wa mijin na ta a siyasance.

Matsin lamabar da ake wa iyalan Jonathan ya isa haka: MASSOB ga Gwamnatin Tarayya

Matsin lamabar da ake wa iyalan Jonathan ya isa haka: MASSOB ga Gwamnatin Tarayya

KU KARANTA: Ma'aikaciyar jinyan Asibiti ta hada baki da wata mata domin sayar da jariri

A cewar Madu, Gwamnatin ta na tunanin idan ta garkame Patience to lallai siyasar mijin na ta zai durkushe. Ya kuma ce kasancewar Patience 'yar kabilar Igbo ce, tozarcin da ta ke fuskanta ba komai ba ne illa tsabar kiyayya ga 'yan kabilar da Gwamnatin Buhari ke yi.

Ya kara da cewa, akwai masu rike da mukamai a wannan Gwamnatin da dama wadanda su ke wasan kura da dukiyar al'umma, amma ko kadan ba a taba bincikar su ba. Haka zalika ba Patience ce kadai daga cikin Tsaffin Matan Shuwagabannin Kasa da su ka barnatar da kudin Kasa ba.

Don haka ne ya yi kira ga 'yan kabilar Igbo da su cire tsoro a ran su, su tsaya tsayin daka don kare 'yan uwan su. Najeriya Kasa ce a suna kawai, in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel