Dole sai gwamnati ta yi la'akari da fushin kowace ƙabila - Inji Obasanjo

Dole sai gwamnati ta yi la'akari da fushin kowace ƙabila - Inji Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, wajibi ne akan gwamnati ta baiwa kowace ƙabila kunnuwan sauraron ƙorafe-ƙorafen su daga dukkan sassan dake fadin ƙasar nan.

Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana cewa hakan shi zai sanya kowace ƙabila jin cewa ita ma tana da muhimmanci a wurin gwamnati.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a jami'ar NOUN dake birnin tarayya, a yayin halartar lacca a taron yaye ɗalibai da aka gudanar a ranar Juma'ar da ta gabata.

Legit.ng da sanadin jaridar The Punch ta fahimci cewa, shugaban jami'ar Igbinedion ta jihar Edo, Farfesa Eghosa Osaghe, shine ya gabatar da laccar akan tsare-tsare na sauyin ƙasa.

Olusegun Obasanjo

Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban ƙasar da ya yi tsokaci kaɗan bayan an kammala laccar ya bayyana cewa, wannan hanya ta sauya tsarin ƙasa zai baiwa dukkan masu ruwa da tsaki a ƙasar nan wata dama ta bayyana ƙorafe-ƙorafen su tare da kawo hanyoyin magance su.

KARANTA KUMA: 'Yan bautar ƙasa biyu sun haihu a sansaninsu na hidima

A nasa jawabin, shugaban jami'ar NOUN, Farfesa Abdalla Adamu ya bayyana cewa, yaye Obasanjo daga jami'ar da kwalin digiri na uku tabbaci ne na cewar babu wanda ya tsofewa neman ilimi.

Ya ƙara da cewa, ya kamata yawan shekaru su daina ƙalubalantar al'umma wajen ci gaba da neman ilimi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel