Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin jihar Katsina ta kara kudaden agaji da ta ke ba ‘yan bautar kasa (NYSC) da aka tura zuwa jihar da kimanin kashi 200. Shugaban hukumar kula da harkokin NYSC a jihar ya bayyana cewa kimanin ‘yan bautan kasa 2,200 aka tura zuwa jihar.

Gwamnatin jihar Katsina ta kara kudaden agaji ga ‘yan bautar kasa (NYSC) da aka tura zuwa jihar da kimanin kashi 200, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari , Alhaji Aminu Ibrahim, shugaban hukumar kula da harkokin NYSC a jihar ya bayyana wannan a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu a Katsina.

Ibrahim, wanda ya wakilci gwamna Aminu Masari na jihar a bikin bude rukuni na ‘Batch ‘B’ Stream II’, wanda kuma shi ne babban mashawarci ga gwamna a kan ci gaban matasa ya bayyana cewa kimanin ‘yan bautan kasa 2,200 aka tura zuwa jihar.

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200
'Yan bautan kasa, NYSC

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ba da fifiko a kan harkokin jin dadin ‘yan bautan kasar da aka tura a jiharsa. Kuma ya yi alkawalin samar da ingantaccen tsaro ga mambobin NYSC a duk fadin jihar.

KU KARANTA: 'Yan bautar ƙasa biyu sun haihu a sansaninsu na hidima

Masari ya bukaci dukkan jami'an tsaro da su tabbatar da tsaro a sansanin NYSC har zuwa karshen shirin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel