Ina da yaƙinin Buhari zai haɓaka tattalin arzikin Najeriya - Oshiomhole

Ina da yaƙinin Buhari zai haɓaka tattalin arzikin Najeriya - Oshiomhole

Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa yana da cikakken yaƙini akan gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da kuma jam'iyyar APC wajen sauke nauyin dimokuraɗiya ga 'yan Najeriya tare da inganta tattalin arziki.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne, Oshiomhole ya bayyana hakan a yayin karɓar baƙuncin wani tsohon ɗan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Mathew Iduroyikemwen, da kuma Honarabul Ehiozuwa Agbonayinma, mai wakiltar ƙananan hukumomin Egor da kuma Ikpoba Okha a majalisar tarayya, wanda ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC tare da dubunnan magoya baya.

Tsohon gwamnan jihar Edo; Adams Oshiomhole

Tsohon gwamnan jihar Edo; Adams Oshiomhole

Tsohon gwamnan yake cewa, tsarin aiwatar da sake gina Najeriya ba zai yiwu cikin dare ɗaya ba, duba da irin rugu-rugun da jam'iyyar PDP ta yiwa ƙasar, saboda haka sake gina ta ba abu ne ƙanƙani ba.

KARANTA KUMA: 'Dimuwa yayin da aka nemi shanu 200 aka rasa a jihar Filato

A kalamansa, "tabbas shugaba Buhari yana iyaka bakin ƙoƙarinsa, kuma ina da cikakken yaƙini tare da tabbaci a kansa da kuma ƙasar mu ta Najeriya. Dole ne sai mun dakatar da masu wawuson kuɗin ƙasar tare da hukunta su."

Legit.ng da sanadin jaridar Daily Trust ta fahimci cewa, Oshiomhole ya kuma janyo hankalin ɗaukacin al'ummar Najeriya wajen ƙauracewa masu kira akan rarrabuwar kawuna ta fuskar addinai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel