Rashin tausayi: An yi wa wata mata fyade, tana tsaka da jego

Rashin tausayi: An yi wa wata mata fyade, tana tsaka da jego

- Mai jego dai ita ce wadda bata dade da haihuwa ba, wadda ake kula da ita kamar maras lafiya

- A kasar Kenya aka aikata mummunan aikin

- A babban asibiti na kasar, gwamnati ta bude bincike

Rashin tausayi: An yi wa wata mata fyade, tana tsaka da jego

Rashin tausayi: An yi wa wata mata fyade, tana tsaka da jego

Gwamnatin kasar Kenya tayi Alla-wadai da rahotannin yade da ake samu kan yi wa masu ciki fyade a asibitocin kasar, kuma ma wai masu sabon jego aka fi yiwa shi.

Minitan Lafiya, Cleopa Mailu, da kungiyoyin kishin mata, sun yi Allah-wadai da kuma kafa damba ta bincike kan yadda ake samun wannan danyen aiki.

DUBA WANNAN: Kotu ta kwace dukiyar Adamu Muazu ta baiwa gwamnati

Mr Mailu ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa,"Yana sane da zargin da ake na yi wa wasu mata da suka yi sabuwar haihuwa fyade a hanyarsu ta fitowa daga dakin haihuwa". Kamar yadda batun yake ta yawo a shafukan sa da zumunta da muhawara.

Wani mai amfani da shafin Facebook ya bayyana cewa "an far wa masu jegon ne a hanyarsu ta zuwa wurin jariran nasu don su ba su nono, inda aka ajiye jaririn a wani gini na dabam.

"Samun tsaro muhimmin al'amari ne musamman ga matan da jariransu suke dakin rainon yara. Dakin rainon jariran na kasa ya yin da dakin masu haihuwar yake hawa na uku.

"Matar ta tafi ne zata ba wa jaririnta nono misalin uku na dare. Ihun da matar tayi ne kawai ya ceceta.

"Anyi wa matar tiyata ne aka cire mata 'yan biyu, amma ba ta gama warkewa ba. Kuma irin wannan matan na bukatar kariya," in ji sakon na Facebook.

Batun ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta daga wurin mutanen da abun ya shafa ko suka san wadanda abun ya faru da su.

An samo wannan labari ne daga BBC Hausa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel