Labarin yadda George Weah ya zama shugaban kasa daga rayuwar talauci

Labarin yadda George Weah ya zama shugaban kasa daga rayuwar talauci

- George Weah kafin zama shugaban kasa, shahararren dan kwallon duniya ne a Turai

- Kafin zamansa dan kwallo dan talakawa ne da ya taso a lungunan talakawa a Monrovia ta Liberia

Labarin yadda George Weah ya zama shugaban kasa daga rayuwar talauci

Labarin yadda George Weah ya zama shugaban kasa daga rayuwar talauci

George Weah shine zababben shugaban kasa a Liberia, kuma ya kayar da tsohon mataimakin shugaba mai barrinn gado Ellen Johnson Sirleaf, wadda a baya ta kayar da shi a zaben shugaban kasa, duk da cewa anyi zarge-zargen magudi.

George Weah dan talakawa ne da ya taso kamar almajiri a lungunan Monrovia ta kasar Liberia, kuma ya koyi kwallo kamar yadda kowa yake yi a da ta 'yar tule.

Ya sami zama zakara a Turai inda ya ci gasar kwallon kaffa da yawa a kulob dinsa da ya taka wa leda.

DUBA WANNAN: Fyade ya koma kan masu jego a kasar Kenya

Ya zama dan wasan duniya a Arsenal karkashin Arsene Wenger, tun yana dan shekariu 21 da haihuwa.

Ya bugawa kasarsa kwallo, kafin zuwansa Turai, inda yayi wasa da Monaco, Arsenal, AC Milan, Chelsea, da ma Paris-St-Germain.

Ya bada agaji sosai ga kasarsa da dukiyarsa wadda ya tara tun kafin shigarsa siyasa a 2005, inda masu hamayya suka ce jahili ne da bai je makaranta ba.

Ya zama dan kwallo na farko a Duniya da kwallonsa ta kaishi ga ofishi mafi girma a irin kasarsa. Pele da Romario dai a kasar Brazil sun yi siyasa, amma a matsayin minista kawai suka ci birki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel