Aisha Buhari ta wallafa bidiyon Sanatocin da suka soki gwamnatin tarayya

Aisha Buhari ta wallafa bidiyon Sanatocin da suka soki gwamnatin tarayya

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha ta wallafa bidiyon sanatoci biyu dake sukar gwamnatin tarayya a shafinta na Twitter @aishambuhari a ranar Juma’a, 19 ga watan Janairu.

A ranar Laraba, Sanata Isah Misau dake wakiltan Bauchi ta tsakiya a majalisar dokokin jihar ya caccaki nadin darakta janar na hukumar liken asiri da akayi inda ya nei sanin ko ya cancanci hawa wannan mataki.

Aisha Buhari ta wallafa bidiyon Sanatocin da suke sukar gwamnatin tarayya

Aisha Buhari ta wallafa bidiyon Sanatocin da suke sukar gwamnatin tarayya

Har ila yau Aisha Buhari ta sake wallafa wani bidiyo na sanata mai wakiltan Bayelsa na gabas, Ben Murray-Bruce, inda yake sukar gwamnatin tarayya tare da ikirarin cewa Najeriya ta kasance kasa mara doka.

KU KARANTA KUMA: Nejeriya ta samu gagarumin ci gaba a fannin noma - Inji shugaba Buhari

Wannan sune abu na farko da uwargidan shugaban kasar ta wallafa a shafinta Twitter tun bayan gaisuwan bikin Kirsimati da tayi a ranar 25 ga watan Disamban 2017.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel