Rundunar Yan Sandan Najeriya ta horas da jami'a 147 dabarun yaki da ta'addanci

Rundunar Yan Sandan Najeriya ta horas da jami'a 147 dabarun yaki da ta'addanci

- Rundanar Yan Sandan Najeriya za horas da jami'an ta 147 da ma na wasu hukumomin tsaron dabaru yaki da ta'addanci

- Sifeta Janar na Rundunar Yan Sanda, Ibrahim Idris ya ce an ba su horon ne domin a koyar da su sabbin dabarun inganta tsaro

- Rundunar ta yan Sanda ta kuma ce za ta cigaba da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro don kawar da ta'addanci

A ranar Juma'a ne Sifeta Janar na Rundunar Yan Sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya ce Rundunar ta horas da jami'a 147 dabarun yaki da ta'addanci. Jami'an da suka sami horaswan sun hada da 'yan sanda da kuma jami'an sauran hukumomin tsaro da ke zone 5.

Sifeta Janar na Yan Sandan ya yi wannan bayanin ne wajen kulen wani kwas na kwanaki 5 kan dabarun yaki da wanda aka shirya domin kwamandoji.

Rundunar Yan Sandan Najeriya ta horas da jami'a 147 dabarun yaki da ta'addanci

Rundunar Yan Sandan Najeriya ta horas da jami'a 147 dabarun yaki da ta'addanci
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Kotu ta jaddada umurnin kama Tsohon Gwamnan Jihar Enugu game da cuwacuwan N5.3bn

Sifetan Yan Sandan, Idris wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Yan Sanda na jihar Edo, Mista Johnson Kokumo ya ce rundunar za ta cigaba da hadin gwaiwa da sauran hukumomin tsaro domin yaki da ta'addanci.

A jawabin da ya yai, Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda, Emmanuel Aina ya yi kira ga mahalarta taron maida hankali wajen wanzar da abubuwan da suka koya a kwas din idan sun koma hukumomin tsaron da suke yiwa aiki.

Ya ce horon da aka bawa Jami'an da suka halarci kwas din, ya koyar da mahalartan sabbin hanyoyin da ake fuskanci ababe da ka iya tasowa ba shiri ba tare da samun ruduni kan hukumar tsaron da za ta jagoranci yaki da ta'addancin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel