Yan siyasa na raba kawunan yan Najeriya don son ransu – Gwamnan jihar Ogun

Yan siyasa na raba kawunan yan Najeriya don son ransu – Gwamnan jihar Ogun

Gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, ya tuhumci yan siyasa da raba kawunan yan Najeriya domin son ransu kawai.

Saboda haka, gwamna Amosun ya yi kira ga kafafen yada labarai gabanin zaben 2019 da su duba abun yin a hada kawunan yan Najeriya sabanin rabasu.

Ya yi wannan magana ne a wakshon yan jaridar gidan gwamnatin jihar mai take: “Rawan ganin kafafen yada labarai wajen gina zaman lafiya: 2019 a madubi.

Game da cewarsa, kafafen yada labarai na da rawan takawa matuka. Ya yi kira gay an jarida suyi rubutu akan abubuwan da zasu hada kan kasa da kuma samar da zaman lafiya.

Yan siyasa na raba kawunan yan Najeriya don son ransu – Gwamnan jihar Ogun

Yan siyasa na raba kawunan yan Najeriya don son ransu – Gwamnan jihar Ogun
Source: Depositphotos

Gwamnan ya kara da cewa babu kasar da ta tsira daga kalubale, amma yada maganganun raba kawuna kan zama cikas ga cigabanmu.

KU KARANTA: APC ta bayyana dalilin da ya sa bata gudanar da taronta na kasa tun 2015 ba

Amosun ya kara da cewa yan siyasa na amfani da rabuwan kan mutane, addini, harshe lokacin da zai musu amfani, amma yana kiraga kafafen yada labarai suyi banza da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel