Badakalar N2.1bn: Mai gidan talabijin na AIT, Raymond Dokpesi ya shiga uku

Badakalar N2.1bn: Mai gidan talabijin na AIT, Raymond Dokpesi ya shiga uku

Mai shaida a karar mai gidan talabijin na AIT, Gabriel Agorye, ya bayyana yadda ya cire miliyan N40m daga asusun bankinsa ya baiwa mai gidansa, Raymond Dokpesi.

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC a shekarar 2015 ta kai Dokpesi kara babban kotun Najeriya dake zaune a Abuja akan zargin badakalar N2.1bn wanda ya karba daga hannun tsohon NSA, Sambo Dasuki.

Agorye wanda mai shaida ne a kotu ya bayyanawa kotu cewa shi ma’aikacin Dokpesi na musamman kuma ya yi masa hidindimu.

Badakalar N2.1bn: Mai gidan talabijin na AIT, Raymond Dokpesi a shiga uku

Badakalar N2.1bn: Mai gidan talabijin na AIT, Raymond Dokpesi a shiga uku

Mai shaidan ya kara da cewa an tura wasu kudade asusunsa wanda ya cire kuma ya baiwa Dokpesi.

Yayinda ake tambaya a koti, lauyan Dokpesi, Kanu Agabi, ya bayyanawa kotu cewa Agorye bai san asalin kudinda ya turawa Dokpesi ba. Bai sani ko na halal bane ko kuma sabanin haka.

KU KARANTA: Kotu ta ba EFCC umurnin kama wani tsohon gwamna

Alkalin kotun John Tsoho ya salami mai shaidan kuma ya dakatad da karar zuwa ranan 6 ga watan Fabrairu domin cigaba da karar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel