Zan ziyarci Kano duk da adawa - Kwankwaso

Zan ziyarci Kano duk da adawa - Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso ya karyata rahotannin kafofin watsa labarai na cewa ya soke shirinsa na ziyartan jiharsa a ranar 30 ga watan Janairu saboda rashin lafiya.

Ziyarar nasa ya haifar da tashin hankalin siyasa a jihar inda wasu yan siyasa ke ikirarin cewa Sanata Kwankwaso zai ziyarci jihar ne saboda ya tsokano yan adawansa da kuma gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.

Zan ziyarci Kano duk da adawa - Kwankwaso

Zan ziyarci Kano duk da adawa - Kwankwaso

Kwanakin baya ne yan sanda suka gayyaci wani kwamishinan jihar, da ya bukaci magoya bayansu da su jefi sanatan a duk lokacin da ya ziyarci jihar.

KU KARANTA KUMA: Ortom ya gana da gwamnonin APC ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kama shugaban kungiyar Miyetti Allah

Da yake magana ta bakin mai bashi shawara a kafofin wata labarai, Binta Rabiu, dan majalisan ya ce zai ziyarci Kano kamar yadda aka tsara.

Kwankwaso ya bayyana rade-radin rashin lafiyarsa a matsayin aikin “gwamna Ganduje da yan fadarsa.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel