Ortom ya gana da gwamnonin APC ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kama shugaban kungiyar Miyetti Allah

Ortom ya gana da gwamnonin APC ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kama shugaban kungiyar Miyetti Allah

- Gwamna Samuel Ortom ya gana da gwamnonin Arewa da APC a ranar Juma’a

- A wajen taron gwamnan ya yiwa abokan aikin nasa korafi akan rikicin makiyaya dake afkuwa

- Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kama shugaban kungiyar makiyaya a jihar

A ranar Juma’a, 19 ga watan Janairu gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya gana da gwamnonin arewa da aka zaba karkashin jam’iyyar APC don tattaunawa akan rikicin makiyaya.

A lokacin ganawar da gwanonin arewa, Ortom ya yi korafi game da shugaban kungiyar Miyetti Allah sannan kuma ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kama shugabannin kungiyar, jaridar Punch ta ruwaito.

Har yanzu muna zaman dar-dar – Ortom ga gwamnonin APC

Har yanzu muna zaman dar-dar – Ortom ga gwamnonin APC

Ya ce: “Mun gode ma Allah zaman lafiya ya fara dawowa jihar kadan-kadan amma har yanzu akwai kalubale a nan, mun san cewa nan bada jimawa komai zai zo karshe saboda a koda yaushe mutanenmu na ba jami’an tsaro bayanai masu amfani.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta ba EFCC umurnin kama wani tsohon gwamna

“Bari na fada maku har yanzu mutanenmu na zaman dar-dar saboda irin barazanar da kungiyar Miyetti Allah ke yi wanda ya fara tun watanni bakwai da suka gabata.

“Muna da hujjoji akan su, abunda muke fadi shine gwamnatin tarayya ta kama shugaban kungiyar Miyetti Allah.”

Gwamnonin da suka halarci ganawar sun hada da: Shetima Kashim, (Borno), Simon Lalong, (Plateau), Mallam El Rufai, (Kaduna), Yahaya Bello, (Kogi) da kuma Mohamad Abubakar, (Jigawa) sai kuma mataimakiyar gwamnan jihar Osun Misis Grace Titilayo Tomori.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel