Kotu ta ba EFCC umurnin kama wani tsohon gwamna

Kotu ta ba EFCC umurnin kama wani tsohon gwamna

- Wata babban kotun tarayya ta ba da umurnin kama tsohon gwamnan jihar Enugu

- Ana zargin tsohon gwamnan da laifin zamban kudi naira biliyan 5.3

- Kotu ta kuma ture rokon da ya yi na ta hana hukumar EFCC kama shi

Mai shari’a Chuka Obiozor na babban kotun tarayya dake Legas a ranar juma’a ya bada umurnin kama tsohon gwamnan jihar Enugu, Chimaroke Nnamani bisa zargin rashawa da hukumar EFCC tayi masa.

Mai shari’a Obiozor ya ki amincewa da rokon da lauyan Nnamani, Mista Rickey Tarfa (SAN) yayi, sannan ya nace kan cewa dole tsohon gwamnan ya bayyana a gabanshi dangane da laifin zamba da kudi naira biliyan 5.3.

Kotu ta ba EFCC umurnin kama wani tsohon gwamna

Kotu ta ba EFCC umurnin kama wani tsohon gwamna

Har ila yau mai shari’an ya soke rokon Nnamani dake kalubalantar hukuncin kotu da kuma bukatan a hana hukumar EFCC kama shi.

KU KARANTA KUMA: Allah ya yi: APC ta bayyana dalilin da ya sa bata gudanar da taronta na kasa tun 2015 ba

Lauyan EFCC Kelvin Uzozie ya yi bayanin cewa duk da cewan an shigar da wani roko akan wadanda ake karewa na 3 da 8, har yanzu ba’a kammala sauraron na Nnamani da tsohon mataimakinsa, Sunday Anyaogu ba, wadanda suka kasance na farko da biyu.

Mai shari’an ya daga sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Fabrairun 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel