Allah ya yi: APC ta bayyana dalilin da ya sa bata gudanar da taronta na kasa tun 2015 ba

Allah ya yi: APC ta bayyana dalilin da ya sa bata gudanar da taronta na kasa tun 2015 ba

- Jam’iyya mai mulki ta bayyana ainayin dalilin da ya sa bata gudanar da taronta na kasa ba bayan ta kwashe kusan shekaru uku akan mulki

- Kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa sun jinkirta ne saboda ra’ayin jam’iyyar

- Ya bayyana cewa jam’iyyar zata gudanar da taronta nan ba da jimawa ba

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana dalilin da ya sa bata gudanar da zabenta na kasa ba tunda ta hau karagar mulki a 2015.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kakakin majalisar, Bolaji Abdullahi, bayyana cewa duk da jinkirta taron jam’iyyar na kasa ba abune mai kyau ba, sun jinkirta ne saboda ra’ayin jam’iyyar.

Allah ya yi: APC ta bayyana dalilin da ya sa bata gudanar da taronta na kasa tun 2015 ba

Kakakin jam'iyyar APC, Bolaji Abdullahi

Legit.ng ta tattaro cewa Abdullahi ya zanta da manema labarai a Lagas a ranar Juma’a, 19 ga watan Janairu, tare da alkawarin cewa za’a gudanar da wani taro nan ba da jimawa ba.

KU KARANTA KUMA: Matan Musulmi da Kirista sun gudanar da addu’a na musamman ga Najeria a Kafanchan

Kakakin jam’iyyar ya bayyana cewa jinkirta taron bai saba ma kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba sabanin yadda ake ta yayatawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel