Tsugunni bata ƙare ba: Mayakan Boko Haram sun sake kai farmaki Madagali, 5 sun mutu

Tsugunni bata ƙare ba: Mayakan Boko Haram sun sake kai farmaki Madagali, 5 sun mutu

Kimanin mutane biyar ne suka riga mu gidan gaskiya a wani hari da kungiyar yan ta’adda ta Boko Haram ta kai da safiyar ranar Juma’a 19 ga watan Janairu, a kauyen Kaya dake karamar hukumar Madagali.

Premium Times ta ruwaito harin ya faru ne kwanaki biyu da yan ta’addan suka kai makamancin harin a kauyen Pallam duk a karamar hukumar Madagalin, inda Sojoji da yan farauta suka kasheguda biyu daga cikinsu.

KU KARANTA: Rikicin makiyaya: Kungiyar Gwamnoni Najeriya ta kai ziyarar gani da ido jihar Benuwe

Sai dai majiyar Legit.ng ta yi hira da wani mazaunin kauyen Kaya, wanda ya tabbatar mata cewa a wannan karon babu jami’an tsaro balle su mayar da martini, inda yace tun da misalign karfe 10 na dare yan ta’addan suka far ma kauyen har na tsawon awanni uku, suka kashe mutum biyar sa’annan suka tsere.

Tsugunni bata ƙare ba: Mayakan Boko Haram sun sake kai farmaki Madagali, 5 sun mutu

Mayakan Boko Haram

Da yake jawabi ga majiyar mu, shugaban karamar hukumar Madagli Yusuf Muhammed ya tabbatar da harin, sa’annan yace Sojoji da mafarauta sun bi sawun yan ta’addan. Shima dan majalisa mai wakiltar Madagli ya tabbatar da faruwan harin, inda yace:

“Mutane na sun kira ni da safiyar yau, suka sanar dani cewa Boko Haram sun kai hari kauyen Kaya, sun kashe akalla mutum 5 tare da jikkata wasu, wannan na nufin kenan har yanzu suna da damar kai hare hare a duk lokacin da suka ga dama, duk da nasarar da Sojojin Najeriya suka samu akansu.

“Ka san kauyukanmu basu da nisa da dajin Sambisa, wannan ne ya bay an ta’addan daman ka mana hari. A gaskiya har yanzu Boko Haram na da karfi. Don haka nake kira ga shugaban kasa ya tashi haikan, don kuwa jama’an Michika da Madagli na mutuwa sakamakon hare haren yan taadda.” Inji shi

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel