Liyafar cin abinci: Buhari ya fito ma shuwagabannin APC a mutum, ya bayyana musu dalilin gayyatarsu

Liyafar cin abinci: Buhari ya fito ma shuwagabannin APC a mutum, ya bayyana musu dalilin gayyatarsu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bude ma shuwagabannin jam’iyyar APC da suka amsa goron gayyatar da yayi musu zuwa fadar shugaban kasa cikinsa, inda ya shaida musu bai manta da su ba.

Duba da batutuwan da ake yamadidi na cewa Buhari bayan daukan mataki kan wasu lamurra nan da nan, shugaban yace yana yin haka ne don yin dogon nazari saboda tabbatarwa bai aikata abin da ba shikenan ba, kamar yadda aka samu matsala a zamanin yana mulkin Soja.

KU KARANTA: Lokaci yayi da shugaba Buhari zai yi murabus daga muƙamin Ministan man fetir na kasa

“Na ga ya dace in kira ku, mu zauna mu ci abinci tare, kuma mu fahimci juna, ina tabbatar muku cewa yadda kuka same ni a nan, ina sane da dukkanin matsalolin Najeriya, a koda yaushe ina nazari, kafin na dauki mataki, tare da waiwayen abubuwan da suka faru a baya.

Buhari ya fito ma shuwagabannin APC a mutum, ya bayyana masa dalilin gayyatarsu

Buhari

“Ni da kai na yanke shawarar na sake tsayawa takara, don haka na bana saurin gudanar da wasu abubuwa har sai na gamsu hakan ne mafita, kuma sai hankalina ya kwanta da wannan mataki.” Inji Buhari.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito shugaban yana tabbatar ma shuwagabannin jam’iyyar cewa ba zai taba mantawa da gudunmuwar da suka bashi ba a lokacin takarar neman kujerar shugaban kasa.

Buhari ya fito ma shuwagabannin APC a mutum, ya bayyana masa dalilin gayyatarsu

Buhari da Kwankwaso

“Na gode muku kwarai da kuka amsa wannan gayyatar, ina baku tabbacin idan kuka ji ban nemi ku ba, ko ban kira ku ba, ba wai don manta da ku bane, ko na manta da gudunmuwar da kuka bani tun bane a shekarun baya.” Inji Buhari, kamar yadda majiyar Legit.ng ta jiyo shi.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun, Sakataren jam’iyyar APC,Mai Mala Buni, tsohuwar yar gwagwarmaya Naja’atu Muhammad, tsohon gwamnan jihar Abia,Orji Uzor Kalu.

Sauran sun hada da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Segun Oni, tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani, tsohon gwamnan jihar Nassarawa, Abdullahi Adamu, Sanata Aliyu Wammako, Abba Kyari da kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel