'Yan bautar ƙasa biyu sun haihu a sansaninsu na hidima

'Yan bautar ƙasa biyu sun haihu a sansaninsu na hidima

A yayin gudanar da bautar ƙasa wasu mata biyu masu juna biyu, sun haife 'ya'yan cikinsu a sansanin hidima na Iseyin dake jihar Oyo kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A ranar Juma'a ta yau, shugabar masu kula da 'yan bautar ƙasa ta jihar Oyo, Misis Ifeoma Anidobi, ta bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a birnin Ibadan, inda tace iyayen sun haife kyawawan jarirai mata biyu.

'Yan bautar ƙasa

'Yan bautar ƙasa

Anidobi ta bayyana cewa, an haifi jariran ne a ranar talatar da ta gabata, wadda ita ce ranar farko ta fara faɗakar da masu yiwa ƙasa hidima dangane da yadda zasu bautawa ƙasar su.

KARANTA KUMA: Jihohi hudu sun baiwa gwamnatin tarayya goyon bayan haƙo man fetur a Arewa

Shugabar ta bayyana farin cikin ta dangane da yadda iyayen suka sauka lafiya ba tare da samun wata tangarɗa ba.

Kamfanin dillancin labari na Najeriya wato NAN ya ruwaito cewa, an rantsar da 'yan bautar ƙasa guda 2, 294 a sansanin hidimar na Iseyin a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, inda 700 daga cikinsu suka zo daga jihar kwara da kuma 645 daga jihar Ogun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel