Rashin gaskiya gami da yaudara sun ɗebo wa wani ɗalibi ruwan dafa kansa a Abuja

Rashin gaskiya gami da yaudara sun ɗebo wa wani ɗalibi ruwan dafa kansa a Abuja

Wata kotu dake zamanta a unguwar Kubwa ta birnin tarayya, ta zartar da hukuncin ɗauri na watanni huɗu akan wani ɗalibi, Aonover Iorwuese bisa laifin yaudara da halin bera.

Kotun ta tabbatar da zargin tare da hukunta ɗan asalin jihar Benuwe mai shekaru 27 da laifin yaudarar mutane da kuma sace musu kuɗaɗe.

Iorwuese ya roƙi sassaucin kotu da cewar kuskure ne kuma ba zai ƙara ba.

Alƙalin kotun, Muhammad Marafa, ya baiwa ɗalibin zabin biyan tara ta naira dubu 40, ya kuma gargaɗe shi akan kauracewa aikata laifi a lokuta na gaba tare da kasancewa mutum nagari.

Rashin gaskiya ta jefa wani ɗalibi a gidan kaso

Rashin gaskiya ta jefa wani ɗalibi a gidan kaso

A yayin shigar da kara, jami'in ɗan sanda Babajide Olanipekun, ya shaidawa kotun cewa, wata mata Mary Abraham ce tayi ƙarar ɗalibin a ofishin su na Kubwa a ranar 13 ga watan Janairu.

KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun harbe wani jami'in tsaro a jihar Katsina

Legit.ng da sanadin jaridar Daily Trust ta fahimci cewa, ɗalibin ya yaudari Mary ne ta hanyar sulalewa da katin ta na ATM bayan yayi basajar taimakon ta wajen zarar kudi a banki, inda bayan wasu lokuta yayi yunƙuri amfani da wannan kati ashe jami'ai sun kafa masa tarko kuma ya afka.

Babajide ya bayyana cewa, jami'ai sun cafke ɗalibin ne tare da katunan ATM har guda 30 na bankuna daban-daban, wanda ya sabawa sasuka na 79, 322 da kuma 287 na dokar ƙasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel