'Dimuwa yayin da aka nemi shanu 200 aka rasa a jihar Filato

'Dimuwa yayin da aka nemi shanu 200 aka rasa a jihar Filato

Al'umma sun ɗimauta hedikwatar dakarun haɗin gwiwa a ranar alhamis ɗin da ta gabata, a yayin da ɓarayin shanu suka yi awon gaba da shanu 209 a jihar Filato.

Kwamandan rundunar Manjo Janar Anthony Atolagbe, shine ya bayyana hakan da cewar, an nemi shanu 200 an rasa amma an gano 100 daga ciki tare da guda 20 da aka tsinto gawarsu.

Ya ƙara da cewa, akwai wasu mutane dake hannu a yanzu da ake zarginsu da aikata laifin, sai dai kakakin rundunar, Manjo Umar Adams, ya bayyana cewa babu wanda aka kama.

Shanu

Shanu

Jaridar The Punch ta ruwaito da sanadin wata majiya mai rauni cewa, kimanin mutane 20 sun shiga hannu da ake zarginsu da laifukan satar shanu, waɗanda suka haɗar da ƙabilun Hausawa, Fulani da kuma wasu ƙabilu a jihar ta Filato.

KARANTA KUMA: Gobara ta lashe gidan mataimakin gwamnan jihar Imo

A wata sanarwa ta shugaban rundunar, Birgediya Janar A.M Bello ya bayyana cewa, babu shakka akwai mutanen da ake zargi da suke hannu a yanzu.

Ya ƙara da cewa, cikin akasin rahotanni, babu wata ɗimuwa cikin jihar Filato duk da barazanar ƙungiyar Miyetti Allah akan sai sun mayar da martanin harin da aka kaiwa 'yan uwansu da kuma sace musu shanu 350 a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel