Daliban Jami'ar Jihar Osun sun yanke jiki sun fadi a cikin aji

Daliban Jami'ar Jihar Osun sun yanke jiki sun fadi a cikin aji

- Daliban da su ka sume 'yan matakin 300 ne na fannin kiwon lafiya da ke harabar Osogbo na Jami'ar

- Shugaban Jami'ar, Farfesa Labo Papoola, ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin

- Sun sume ne sakamakon shakar iskar carbon dioxide da su ka yi wanda ya huro daga fasasshiyar gwangwanin kashe wuta

Akalla mutane 12 ne daga cikin daliban harabar Osogbo na Jami'ar Jihar Osun, su ka yanke jiki su ka fadi yayin da su ke karban karatu a cikin aji. A yayin da wadansu su ka ce ba a san musabbabin sumar ta su ba, rahotanni daga dalibai sun banbanta.

Wadansu sun ce daliban sun shaki iska mai guba ne da ya shigo cikin ajin daga dakin bincike da sinadarai. Wadansu kuwa cewa su ka yi iskar Carbon dioxide ne su ka shaka. Iskar ta huro ne sakamakon fashewar gwangwanin kashe wuta da ke dauke da iskar.

Daliban Jami'ar Jihar Osun sun yanke jiki sun fadi a cikin aji

Daliban Jami'ar Jihar Osun sun yanke jiki sun fadi a cikin aji

DUBA WANNAN: Kwana daya bayan taron sulhu a Ekiti, Makiyaya sun kashe wata mata mai ciki

Kasancewar ajin ta cika makil da dalibai har ya kasance babu wurin zama, ta sa wani dalibi ya zauna dirshen a kan gwangwanin na tsawon lokaci mai tsawo, wanda hakan shi ya janyo fashewar gwangwanin.

Shugaban Jami'ar kuwa, Farfesa Labo Papoola, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce daliban na fannin kiwon lafiya ne. A cewar sa, mutane 20 ne su ka cutu da iskar, wasu kuma sun samu rauni sakamakon firgicin da karar fashewar gwangwanin ya haifar.

Tuni dai a ka aika da daliban asibiti don duba su. An kuma yi dacen babu wata matsala tare da su. Wannan lamari ya faru ne a ranar Alhamis din da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel